Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya a shirye ta ke ta cike gibin iskar gas a nahiyar Turai da yakin Rasha da Ukraine ke yi sanadiyar lalatawa
Shugaban ya yi magana a ranar Alhamis a cikin sanarwarsa game da bangarorin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Portugal da aka gabatar a fadar shugaban kasar da ke Lisbon.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, ya ce Najeriya a shirye take da ta kasance cibiyar kasuwanci maras shinge ta Afirka (AFCFTA).
Ya bukaci kasar Portugal da ta dauki Najeriya a matsayin abokiyar ta mai kima da aminci a Afirka a daidai lokacin da duniya ke cikin mawuyacin hali.
Shugaba Buhari ya bayyana wasu muhimman fannoni guda biyar na hadin gwiwa da za su ciyar da kasashen biyu gaba, wadanda suka hada da mai da iskar gas, masana’antar yawon bude ido da karbar baki, zirga-zirgar jiragen sama, tsaro da hukumar hadin gwiwa.
Dangane da batun man fetur da iskar gas kuwa, shugaba Buhari ya ce da yakin Rasha da Ukraine, karin hadin gwiwa a fannin mai da iskar gas a tsakanin kasashen biyu ya zama muhimmi wajen kaucewa matsalar bukatu da wadata, duk da cewa Najeriya ce ke kan gaba wajen samar da iskar gas akan Portugal.
A yayin ziyarar tasa shugaban ya jaddada bukatar sanya hannu kan yarjejeniyar ayyukan jiragen sama (BASA) da kuma gaggauta kafa hanyar zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Buhari, yayin da yake jaddada aniyar Najeriya na yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel, ya shaidawa takwaransa na kasar Portugal cewa Najeriya za ta yi maraba da tallafin da kasar ke yakamata ta samu daga Gwamnatin Portugal ta hanyar leken asiri da musayar bayanai, makamai da horar da jami’an tsaro na kasashe mambobi.
Ya kuma jaddada bukatar kafa kwamitin hadin gwiwa don inganta ci gaban manufofin huldar dake tsakanin kasashen biyu.