Dan wasan gaba na kungiyar Al Nassr, Cristiano Ronaldo, ya mayar da martani kan wasan da suka tashi babu ci 0-0 da Paris Saint-Germain a wasan sada zumunci.
Ronaldo ya kasa zura kwallo a raga yayin da kungiyar Saudi Arabia Pro League ta rike kofin Ligue 1.
KARANTA WANNAN: NPFL: Kano Pillars Ta Nada Sabon Koci
Bayan wasan, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya shiga shafin Instagram inda ya rubuta sako ga magoya bayan Al-Nassr.
Dan wasan mai shekaru 37 ya yaba da kwazon PSG a wasan kuma ya gode wa magoya bayansa saboda kyakkyawar tarbar da suka yi masa a Japan.
Ronaldo ya rubuta: “Kyakkyawan rawar da suka taka a kan wata kungiya mai karfi.
“A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar kakar wasa! Kyakkyawan maraba daga magoya baya a nan Japan. ”
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: PSG Ta Sanya Dan Wasa Mbappe A Kasuwa
Paris Saint-Germain ta cire Kylian Mbappe daga ziyarar da za ta yi zuwa kasar Japan.
Zakarun Ligue 1 yanzu sun sanya dan wasan mai shekaru 24 a duniya a kasuwa.
Fabrizio Romano wanda ya kasance kwararre a harkokin musaya ne ya bayyana hakan.
“An bar Kylian Mbappé daga cikin ‘yan wasan Paris Saint-Germain don rangadin kakar wasa a Japan.
“PSG ta yanke wannan shawarar ne a daren yau juma’a.
“Ku fahimci PSG tayi la’akari da Mbappé A MATSAYIN NA SAYARWA,lamarin ya fara daga yau.
“Paris Saint-Germain tana jin Kylian Mbappé yana son barin matsayin kyauta a shekarar 2024 – duk da bai yi magana da kowa ba tukuna duk da sanarwar jami’an Al Khelaifi.
“PSG ta yanke shawarar fitar da Kylian daga yawon shakatawa na Japan,” Romano ya wallafa a shafinsa na Twittya a daren yau Juma’a.