Shahararren ɗan wasannan wato Christiano Ronaldo yaci gaba da kafa tarihi wajen taimakawa ajefa ƙwallaye a gasar zakarun nahiyar turai. Domin kuwa ko a daren jiya ya sake taimakawa a wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta caskara Ferencavaros daci 4 da 1.
A gasar ta zakarun turai dai akwai jerin ‘yan wasa guda 11 da sukafi taimakawa wajeb jefa ƙwallaye kuma Christino Ronaldo ne a kan gaba inda ya taimaka akaci sau 41.
Ga jerin ‘yan wasan kamar haka:
1. Christiano Ronaldo yayi taimaka sau 41.
2. Leonel Messi ya taimaka sau 36.
3. Ryan Giggs ya taimaka sau 31.
4. Angel Dimaria ya taimaka sau 30.
5. Xavi Hernandez ya taimaka sau 30.
6. Inesta ya taimaka sau 29.
7. Neymar ya taimaka sau 27.
8. Karim Benzema ya taimaka sau 27.
9. Fabregas ya taimaka sau 26.
10. Luis Suarez ya taimaka sau 26.
11. Ibrahimovic ya taimaka sau 26.