Gwamnatin Jahar Lagos tace iyalan waɗanda lamarin ruftawar ginin Ikoyi ya rutsa dasu, zasu iya zuwa Asibitin Kula da masu cututtuka na Yaba, domin duba gawarwakin ƴan uwan su da aka gano a cikin ginin.
Za’a gudanar da bincike kafin iyalan su iya tafiya da gawarwakin ƴan uwan na su.
Gwamnatin Jahar tace ta samo gawarwaki 38 daga cikin ginin, a yayinda shirin gano gawarwakin yakai cikin kwanaki 4 a ranar Juma’a, tana mai jaddada cewa iyalai sun shigar da sunaye 32 na ƴan uwansu da suka rasa a ginin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan siyasa ne ke kawo tsaiko ga shirin sasanci da ƴan bindiga a Zamfara — Cewar Matawalle
Kwamishinan Yaɗa Labaru da Dabaru na Jahar Mr. Gbenga Omotoso ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a ranar Juma’a, inda ya ƙaryata rahoton dake cewa masu gano gawarwakin sun daina aikin da suke yi na ceto a ranar Alhamis.
Yace “a halin yanzu, mun samu gawa 38 da kuma mutum 9 daga ciki wanda suka rayu, wasu gawarwakin an shirya su domin ganewa daga iyalan su.
“Gawar da baza’a iya ganewa ba, zamu gudanar da gwajin ƙwayoyin halitta domin a gane su. Akwai dokoki a wajen bayar da gawar ga Al’umma.
Comments 1