Shafin ???????? @HaramainInfo dake Twitter ya labarto cewa rukunin farko na Alhazan bana na 2020 sun iso birnin Jeddah domin sauke farali.
Maniyyata hajjin na bana sun sauka ne a filin sauka da tashi na King Abdulaziz International Airport, inda hukumomi da jami’an lafiya suka tarbe su domin duba lafiyarsu domin kariya daga yada cutar annobar korona.
Idan ba ku manta ba, A cikin watan Yunin 2020 ne mahukumta Saudiyya suka ce mazauna kasar ne kawai cikinsu har da ‘yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta za a bari a bana su yi aikin Hajjin saboda annobar cutar korona.
A bana mutum dubu goma ne kawai za su yi aikin hajji.