Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da karar wani babban dalibin kwalejin ilmin addinin musulunci ta Elkanemi Maiduguri da ya sara masa wuya dan shekara 11 dan karammin kwalejin ilimin tauhidi da ke Maiduguri.
Matashin mai shekaru 11 wanda a halin yanzu yana kwance a sashin kula da lafiya na asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, kamar yadda rahotannin da ke cewa babban dalibin ya ladabtar da shi saboda ya ki yi masa aiki.
Kwamishinan jihar Abdu Umar ya kuma tabbatar wa manema labarai wani ma’aikacin NGO da ya yi wa yarinya ‘yar shekara 18 fyade wanda ya yi sanadin kisa.
Ya lura cewa ana cigaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba za a sanar da manema labarai.