Rundunar Sojin Ƙasa ta musamman ta Operation Safe Haven na aikin tabbatar da zaman lafiya a Jahar Filato, inda ta gargaɗi waɗanda ke ruruta wutar faɗace-fadace a Jahar dasu daina, ko su fuskanci hukunci.
Kwamandan Rundunar Manjo-Janar Ibrahim Ali, wanda yayi jawabin hakan bayan ya karɓi rahoton wani kwamiti na musamman akan samar da zaman lafiya da rundunar ta kafa, yace nan bada jimawa ba za’a gano masu aikata laifin.
Ali ya kuma gargaɗi Shuwagabannin al’umma musamman waɗanda suke ɓoye ƴan ta’adda dasu daina hakan, ko su fuskanci hukuncin doka.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Daliban Makarantar Gandun Daji A Jihar Ondo
“Ina son in tura gargaɗi mai ƙarfi ga masu ruruta wutar faɗace-fadace, da masu baiwa ƴan ta’adda mafaka, inji shi
Ya kuma bayyana cewa zasu ɗauki hukunci mai tsanani akan su ba tare da duba matsayi ko kuma wani abu nasu a cikin al’umma.
Ali ya kuma buƙaci al’umma, da masu riƙe da Sarautun gargajiya, da Shuwagabannin addini a Jahar, dasu goyi bayan rundunar wajen samar da zaman lafiya a dukkanin sassan jahar.