Rundunar sojin Kasar nan ta ce ta kama mutane 12 a yankin Kudu maso yammacin Najeriya, bisa laifukan sojan gona
.
Kwamandan dake kula da shiyar Manjo Janar Umar Thama Musa ne ya bayyana hakan Inda ya ce, an kama wadanda ake zargi ne a jihohin Legas da Ogun inda suke sanye da kakin rundunar sojin.
Ya Kara da cewa, ko a watan Janairun shekarar da ta gabata, sai da aka kama akalla mutane 150 da aikata irin wannan mummunan laifi.
Sojojin bogin dai ansha kamasu da aikata haramtattun aiyukan kamar kafa shingen binciken ababen hawa, domin amsan nagoro a hannun direbobi.