A ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, shekarar 2021, shelkwatar rundunar tsaro ta Najeriya, ta bayyana nasarar da ta samu a kan yan bindiga a jihar Zamfara.
Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe akalla yan bindiga 123 a jihar ta Zamfara.
Rundunar Operation Hadarin Daji sun yi farmakk mafakar yan bindigan a dajin Dansadau, jejin Kwiambana, dajin Sabubu da kuma na yankin Dudufi.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Darektan rikon kwarya na yada labaran shelkwatar rundunar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan, da yake jawabi a jiya Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sanda ta Garkame Sakatariyar Yan jarida a Rivers
Inda ya ya ke cewa, an samu wannan nasara ne a makonni biyu da suka gabata.
Kazalika ya ce, “Tsakanin 2 zuwa 6 ga watan Agustan 2021, sojojin saman, da Operation Hadarin Daji sun kai wa yan bindiga hare-hare a inda suka fake a kudancin garin Dansadau, Arewa da Dajin Kwiambana, da kuma Arewacin dajin Sububu, da kauyukan Dudufi a yankin Faru, karamar hukumar Muradun, duk a dai a jihar Zamfara.” inji shi.
“Luguden wuta ta saman da aka kai, ya yi sanadiyyar ruguza gidajen Yan bindigan, har da wani daga cikin shugaban yan bindigan, Halilu Tubali, yayin da su ke yin wani taro.” a cewar shi.
“Hare-haren saman da kuma guduma war da sojojin kasa su ka bada, ya taimaka wajen ganin bayan yan bindiga 123, tare da rusa masu kayan gidajen su.” kamar yadda ya bayyana.