Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike bayan an kama wasu jami’an sojoji biyu kan kisan wani malamin addinin Islama a jihar Yobe, Sheikh Goni Gashua.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kennedy Anyanwu ya sanyawa hannu, rundunar ta riga ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Yobe domin bayyana sunayen ‘jami’an sojin da ake zargi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen 2023 Zai Kasance Tonon Silili Ga Rashin Iya Mulkin APC — Tsohon Shugaban PDP
“Bugu da kari kuma, Sashen ya kafa wani kwamitin bincike domin bankado al’amuran da suka shafi wannan lamari mara dadi.
“A karshen binciken, za a sa sojoji su fuskanci fushin dokokin soja da na farar hula.”
“Wannan lamarin abin bakin ciki ne matuka ganin yadda bangarorin suka nuna halin ko in kula game da saba dokoki da ka’idojin aiki na sojoji.”
“Saboda haka, sashen na fatan jajantawa iyalan wanda abin ya shafa da kuma mutanen jihar Yobe nagari tare da yin alkawarin cewa za a yi adalci a kan haka.”
Kisan Gashua
Gidan Talabijin na Channels ya bada labarin kashe Sheikh Goni Aisami-Gashua a ranar Asabar.
An ce malamin ya taso ne daga Gashua zuwa Kano a cikin wata motar safa da maharan suka bi shi.
Wasu mazauna Gashua sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe a Jajimaji mai tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu, ya ce an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47, kuma suna hannun ‘yan sanda a yau.
Gashua dai na daya daga cikin al’ummar jihar da suka fi zaman lafiya, hatta a lokacin da ake fama da rikicin Boko Haram.
A wani labarin kuma Abinda Yaɗa Labaran Ƙarya Kan Najeriya Zai Haifar – NCAC
Darakta-Janar na majalisar kula da fasaha da al’adu ta kasa (NCAC), Otunba Olusegun Runsewe, ya ce yada labaran karya game da Najeriya zai hana masu zuba jari da sauran damammaki masu ma’ana ga kasar.
Da yake jawabi a karshen mako a Abuja a bikin EXPO 2022 na kasa da kasa na INAC karo na 15, ya ce ‘yan Najeriya da su kare martabar Najeriya domin ta samu ci gaba.