Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka yan kungiyar Boko Haram da dama, yayin da suka yi yunkurin kai wani hari a kauyen Rann Shelkwatar Karamar Hukumar Kala Balge dake Jihar Borno.
Cikin wata sanarwa daga Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Birgediya Muhammad Yarima, ya ce rundunar ta yi wani kwantan bauna ne wa mayakan Boko Haram din yayin da suka yi yunkurin kutsawa kauyen.
Kazalika sanarwar ta ce an nasarar karɓe makamai bila’adadin a gurin yayan kungiyar, wadanda suka hada da AK47 da alburusansu.
Baya ga nan kuma ta ce akwai na’urar kakkabe Jirgin yaki da kuma mashin gun.