Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato, Charles Mato Dakat.
Idan dai za a iya tunawa, wasu ‘yan bindiga sun sace Charles Dakat, wani basarake a karamar hukumar Gindiri a fadarsa da misalin karfe 1 na safe.
Sai dai an sake shi da sanyin safiyar Juma’a.
Da yake tabbatar da kama mutanen takwas a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a jim kadan bayan da sarkin ya samu ‘yancinsa, jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Safe Haven’ ya ce, “Yayin da mai rike da sarautun Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, Cif Charles Mato Ya kasance tare da wadanda suka yi garkuwa da shi, kwamandan Operation SAFE HAVEN, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya sanya sojojin da aka tura a Gyanbus cikin jajircewa da kuma sajewa da maharan.
A cewar sanarwar, “Saboda haka, an kama mutane takwas da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane kuma ana yi musu tambayoyi. Bayan wannan cigaban ne, da safiyar yau Juma’a 31 ga Disamba, 2021, masu garkuwa da mutane suka sako babban mai mulki.”
Sanarwar ta kara da cewa “Operation SAFE HAVEN na cigaba da aiki tukuru domin ganin an kama duk wadan da ke da hannu a sace basaraken gargajiyar tare da fuskantar fushin doka.”