‘Yan sandan da ke yaki da ta’addanci sun gayyaci shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Ennahda a Tunisiya, Rached Ghannouchi domin amsa tambayoyi.
Mista Ghannouchi kuma shi ne kakakin majalisar dokokin kasar, wanda shugaba Kais Saïed ya rusa a cikin makon nan – sai dai jagoran Yan adawa yayi Allah wadai da wanna mataki.
A ranar Alhamis din da ta gabata ce hukumar yaki da ta’addanci ta kasar Tunisia ta gayyaci ‘yan siyasa fiye da 30 da suka halarci zaman majalisar dokokin ta yanar gizo, domin nuna rashin amincewa da shugaban kasar.
Wannan zaman dai shi ne na farko tun bayan da shugaba Saïed ya dakatar da majalisar watanni takwas da suka gabata tare da kwace madafun ikon kasar Baki daya.