Jami’an yan sanda a jihar sun ce, sun kama wasu mutune goma sha biyar da a ke zargin yan kungiyar asiri ne, wadanda kuma ake kyautata zaton cewa, daliban Kwalejin kimiyya da fasaha ta Mustapha Agwai dake garin Lafiya ne.
Rundunar yan sandan jihar ta kuma ce, wadanda ake zargin, sun kasan ce barazana ga yankin Ombi dake jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Lere: Engr Ahmed ya kasance Mai jinkan talakawa, cewar Sanata Uba Sani
ASP Ramhan Namsel jami’in hulda da jama na rundunar yan’sandan jihar ne ya bayyana wa mane ma labarai hakan a jiya Lahadi, inda ya ce, ankama dukkannin wadanda ake zargin ne a ranar 12 ga watan Ogustan shekarar nan.
ASP Namsel ya ce “A yunkurin rundunar na ya ki da ta’addanci a fadin jihar Nasarawa, a ranar 10 ga wata Ogustan shekarar 2021, sai ta sami wasu rahotannin sirri, inda wata kungiyar asiri ke yunkurin farmakan abokiyar hamayyar ta, da musalin karfe 12:20 na dare, a garin Lafiya. Wanda hakan yasa Kwamishinan Yan sandan jihar Mr Adesina Soyemi, ya bai wa Tawagar dake yaki da masu asiri da kuma Tawagar dake yaki da masu Garkuwa da mutan wato SWAT, umarnin diranma maboyar Yan kungiyar, dake gini mai numba daya 1, daura da Isah Mustapha Agwai a garin Lafiya, inda nan take, Tawagar ta kama Mutum 15 da ake zargi”.
A cewar shi, Wadanda ake zargin tuni suka amince da cewar, su mambobin kungiyar asiiri ce ta Viking/Arobaga da kuma Black Axe.
Kazalika ASP Namsel ya ce, Kwamishinan yan sandan jihar ya ja kunnen masu gidajen haya, kan bai wa yan kungiyar asiri hayan gida, Indan ba haka ba, toh babu shakka zai kama su, domin su kasance izuna a ga wasu mutanan.