By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar Hukumar aikin ‘Yan Sanda za su kammala aikin daukar ma’aikatan ‘Yan Sanda dubu goma (10,000) da za a dauka a shekarar 2020.
Sanarwar da CP Frank Mba, Jami’in hulda da jama’a na runduna shine wanda ya sanar da hakan a ranar Asabar a Abuja yace, “A saboda haka, ana bukatar wadanda suka nemi aikin dasu duba matsayin daukar su a safin hukumar daukar ma’aikata,na www.policerecruitment.gov.ng wanda za a bude daga ranar Litinin, 18 har zuwa Talata, 26 ga Oktoba, 2021.
‘‘Yan takarar da suka cancanta zuwa mataki na gaba na aikin daukar ma’aikata su ne za su je wajen masu kafe dan fitar takardar inda kowa zaiga ranar jarrabawar su wacce dole ne a gabatar da ita a ranar jarrabawar da aka shirya gudanarwa ranar Juma’a, 29 da Asabar, 30 ga watan Oktoba, 2021 a cibiyoyin da aka kebe a fadin kasar nan. Haka kuma an shawarci masu takarar dasu duba imel da lambobin waya don samun sakon sanarwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Rundunar, ta sake nanata cewa aikin daukar ma’aikata kyauta ne kuma ba tare da wani larura ba, ya umarci ‘yan takarar dasu kira wannan lambar 08100004507 don ci gaba da bincike game da aikin daukar ma’aikatan ‘yan Sanda afadin kasar”