Wasu ‘yan ta’adda sun sake kai wani hari a unguwar Gwantu Kurmi hedikwatar karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da wani dalibin jami’ar jihar Kaduna da wani mai wucewa, yayin da wani mutum guda ya samu rauni sakamakon harbin bindiga.
Shugaban kungiyar Gwantu wato People’s Progressive Union a Turance , Prince Bala Audu, wanda ya tabbatar wa LEADERSHIP afkuwar lamarin a ranar Litinin, ya ce Joshua Victor Arumbus na karatu ne a Sashen Gine-gine na Jami’ar Jihar Kaduna, da wani mai wucewa Mista Simon, yayin da aka yi garkuwa da su. mutum daya ya samu munanan raunuka.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne a ranar Asabar da misalin karfe 9:13 na dare, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Audu ya yi tir da yadda matsalar sace-sacen mutane ke karuwa a karamar hukumar Sanga, yayin da ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen amsa kiraye-kirayen da al’uma ke yi musu.
“Abin takaici ne cewa wannan lamari, Kuma ya faru ne mai wuri dake da nisan kilomita daya daga Ofishin yan sanda ta Gwantu da kuma hedkwatar rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke Gwantu,” Audu ya ce, yayin da yake kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta dauki tsattsauran mataki wajen dakile matsalar tsaro Wanda ke ci gaba da zama barazana ga jihar.
Audu ya kuma bukaci hukumomin kananan hukumomin da su samar da wata runduna a kowace al’umma dake cikin karamar hukumar da za ta yi amfani da duk wata hanya ta doka wajen kare al’umar yankunan su.