Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta kama akalla ‘yan jari bola guda 98 da aka fi sani da ‘baban bola’ bisa zargin satar kadarorin mazauna garin.
Da yake baje Kolin wadanda ake zargin a ranar Litinin a hedikwatar rundunar, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan, DCP Ben Igwe, ya ce Abuja ba ta kowa ba ce, ya bayyana cewa rundunar za ta tasa keyar wadanda ake zargin zuwa jihohinsu na asali.
DCP ya shaida wa manema labarai cewa wasu baragurbin mutane sun yi ta kutsawa cikin babban birnin Tarayya Abuja, inda ya bayyana cewa rundunar na kokarin kawar da irin wadannan mutane daga Abuja.
Ya ce, “Abuja ba ta kowa ba ce. Mun umarce su da su je inda ya kamata.
“Muna kokarin ganin mun kawar da su daga FCT. Za mu ci gaba da yin haka kuma ba za mu ja da baya ba.
“Mun kwato musu abubuwa da dama da bai kamata su yi barna ba. Suna satar kadarori yayin da suke iƙirarin yin sana’a.
“Mun bukaci su koma garuruwan su. Mutane da yawa sun yi ta tururuwa zuwa cikin Abuja Kuma wasu daga cikinsu suna zuwa da mugun nufi. Duk lokacin da kuka gansu, ku sanar da mu.
“Muna kai su kotu domin tabbatar da an yi adalci. Muna da matsala mai tsanani a yanzu saboda korafe-korafe daga wurare da yawa “