Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ayyana ranar Litinin 1 ga watan Al-Muharram na shekarar Hijirah 1443 AH, wacce ta yi dai dai da 9 ga watan Ogustan shekarar 2021, a matsayin ranar hutu aiki, a daukacin fadin jihar.
Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanar wa da tasami sa hannun Kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba, inda ya bayyana cewa, ranar hutun na daga cikin murnar shiga sabuwar shekarar Hijrah ta 1443 AH.
Kazalika gwamnan jihar ya kuma bukaci Ma’aikatan jihar, da su yi amfani da wannan ranar hutu, wurin yi wa kasa addu’a, kan shanyo matsalolin tsaro, da ya addabi fadin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an soji sun dakile harin yan bindiga a Kaduna, Kuma sun ceto mutun 6
Ganduje ya kuma taya al’umar Musulmai murnar zagawowar sabuwar shekarar ta Musulunci.
Kazalika sanarwar ta kuma bukaci al’uma ba ki daya, da su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya, wurin magance kalubale da kuma matsalolin da kasar nan ke fuskanta.
A wani labarin Kuma Mai kama da wannan.
Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnan Osun ya ai’yana Litinin a matsayin ranar hutu
Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun ya bayyana ranar Litinin 9 ga watan Ogustan shekarar nan, a matsayin ranar hutu, na shiga sabuwar shekarar addinin Musulunci wato Hijrah 1443 AH.
Bayanin hakan na kunshene a cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Tajudeen Lawal, da ya fitar a yau juma’a a garin Osogbo.
Gwamnan ya kuma ja hankalin dukkannin Musulmai da kuma sauran Mabiya wasu addinai, da su yi amfani da wannan dama, wurin yi wa jihar da ma kasa baki da ya addu’ar fatan samun cigaba mai dorewa.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, sabuwar shekarar Hijira za ta fara ne a ranar Litinin Mai zuwa, wacce ta yi dai dai da 9 gawatan Ogustan shekarar nan da muke ciki.
Comments 1