By Abbas Yakubu Yaura
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samdaddy Anyanwu, a ranar Litinin ya yi kira da a kamo tare da gurfanar da wadanda suka yi garkuwa da ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a zaben fidda gwani da aka kammala a jihar Imo, na mazabar Ngor Okpala a ranar Asabar da ta gabata.
Anyanwu ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Owerri, kan sakamakon zaben fidda gwani.
A cewar sa, sace ma’aikatan wucin gadi na hukumar ta INEC ya nuna yadda tsarin ya tabarbare da kura-kurai.
Sannan Anyanwu ya ce: “Muna so mu yi Allah wadai da sace ma’aikatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a zaben mazabar Ngor Okpala. Mun bayyana a matsayin abin kyama da damfara, sace kayan INEC da wasu ‘yan bangar siyasa da ake zargin suna biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki.
“Satar kayan INEC ya zo ne bayan da labari ya shiga hannun jama’a cewa dan takarar jam’iyyar PDP ne ke kan gaba a kusan dukkanin rumfunan zabe da dakunan zabe a karamar hukumar Ngor Okpala.
“Ga dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Blyden Amajirionwu da ya sha kaye a rumfar zabensa ya tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar PDP, Jeff Nwachukwu da gaske ya ke gaban babban abokin hamayyarsa.
“Muna kira ga jami’an tsaro a jihar da su gaggauta kama wadanda ke da hannu wajen sace kayan zabe tare da yin kira ga magoya bayan PDP da su kwantar da hankalinsu.
PDP, ta ce: “Jam’iyyar ba za ta taba amincewa da wani abu da ya wuce zabe na gaskiya da adalci ba, ko da ina yaba wa jam’iyyar da ta yi watsi da duk wata barazana da APC ke yi na magudin zabe.”