By Abbas Yakubu Yaura
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin dake birnin Beijing ta gargadi ‘yan kasar Sin da kamfanonin dake aiki a nahiyar Afirka kan yin balaguro zuwa wasu yankuna masu hadari a yayin da ake yin garkuwa da ‘yan kasar Sin a Afirka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, a ranar Litinin ya tabbatar da sace wasu ‘yan kasar Sin biyar a jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.Ya kuma bukaci wadanda ke wurare masu hadari da su tashi da wuri daga wajen.
Zhao yace an yi garkuwa da mutanen ne a yayin wani hari da aka kai kan wata mahakar ma’adinan zinari a kauyen Mukera dake gabashin Kongo, ya kara da cewa a wani lamari na baya-bayan nan daya faru a Najeriya, an kuma yi garkuwa da ma’aikatan kasar China uku.
Mai magana da yawun kasar ta sin ya jaddada cewa “akwai manyan hadurran tsaro” a Najeriya da Kongo, kuma wadannan al’amura ba su kasance irinsu na farko ba.
“A baya ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da kuma ofishin jakadancin sun shawarci ‘yan kasar da kada su je wuraren dake da hadari.”
Hakan ya haifar da karuwar kyama ga ma’aikatan kasar Sin masu hannu da shuni da ke aiki a kasashe irin su Kongo mai arzikin albarkatun kasa, inda yanayin rayuwa ya yi tsada.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A shekara ta 2008, tsohon shugaban kasar Congo Joseph Kabila, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da cece-ku-ce ta dala biliyan tara, wadda ta baiwa kasar Sin hakkin hako ma’adinai a kasar, domin samun kudaden gudanar da ayyukan more rayuwa da ake bukata.