By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa dake alaka da sauran laifuka ta Najeriya mai zaman kanta ICPC, ta samu wani injiniya mai suna Dasel Nanjwan a hukumar dake kula da harkokin fitar da kayayyaki a Najeriya da laifi.
Kotun Daukaka Kara ta Calabar ta yanke wa Najwan hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda samunsa da laifin aikata wani sirri na kwangilar na naira miliyan 342 dangane da sauya shaguna da masana’antu a wani ciniki maras shinge a Calabar.
Mutumin da aka yanke wa hukuncin, mamba ne na kwamitin fasaha na gwamnatin tarayya kan wata tattaunawa da kamfanin General Electric Africa kan zuba jari a yankin ciniki maras shinge na Calabar da kuma mai shi kuma shi kadai ya sanya hannu a asusun kamfanin Kwop-ri Services, kamfanin daya yi kwangilar.
Da farko dai hukumar ICPC ta gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban wata babbar kotun birnin Calabar karkashin jagorancin mai shari’a Emily Ibok bisa tuhume-tuhume biyar da suka hada da sanin ya kamata a kan wata kwangilar ta naira miliyan 342 dake da alaka da wani ofis da yake aiki, laifin daya saba wa hukunci a karkashin sashe na 12 na Dokokin Cin Hanci da Sauran Laifukan Dokokin 2000.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wata sanarwa a ranar Litinin data gabata ta bakin kakakin hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua, tace tun farko an sallami mai laifin tare da wanke shi a ranar 19 ga watan Mayu, 2019, amma hukumar ta daukaka kara kan hukuncin.
Sanarwar mai taken ‘Almundahanar kwangilar naira miliyan 342,ICPC ta samu hukuncin daurin rai da rai ga ma’aikacin hukumar dake sarrafa kayayyakin da ake fitarwa a Najeriya, kamar yadda mai shari’a Emily Ibok ta yanke a wata babbar kotu da ke Calabar a ranar 19 ga watan Mayu, 2019, an sallami wanda ake kara daga dukkannin zarge zargen aikata laifin da ake yi masa.
Sai dai kuma “Bata gamsu da hukuncin ba, ICPC ta shigar da kara a sashin Calabar na kotun daukaka kara. Inda Kotun daukaka karar ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai, bayan ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke, sannan kuma ta yanke hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.”