Ɗan wasan tsakiyar tawagar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta ƙasar Jamus, wato Sadio Mane ya shiga cikin tawagar yan ƙasar a gasar kofin Duniya na shekarar 2022 a ƙasar Qatar.
Mane, Mai shekaru 30 a baya an yi fargabar ba zai halarci gasar ba sakamakon raunin da ya samu a wasan da ƙungiyar sa ta Bayern da ta fafata a gasar Bundesliga na karshen mako.
KARANTA ANAN: Kotu Ta Soke Takarar Wasu Yan APC 16 A Jihar Rivers
Tsohon ɗan wasan tawagar Liverpool zai jagoranci ƙasar ta shi a karo na farko a gasar kofin Duniya, cikin fatan ɗorawa daga nasarar da sukayi na zama zakaran kofin nahiyar Afirka na AFCON, da aka kammala a ƙasar Kamaru a shekarar 2021.
Yanzu haka dai kwana 9 ya rage akai ga fara gasar, wadda zata gudana a kasar Qatar.
Yanzu haka dai hukumomin kasar na ci gaba da gyara komai domin abubuwa sun daidai ta.
A wani labarin kuma: Jam’iyyar APGA Ta Yi Alwashi Lashe Zaben Shugaban Kasa A 2023
Shugaban jam’iyyar (APGA) na kasa, Victor Oye, a ranar Juma’ar nan, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
“APGA ba karamar jam’iyya ba ce. Za mu ci zabe a 2023. Za ku gani. Na san za ku yi mamakin yadda abin zai faru. Kada ku manta cewa Allah ne yake yin sarakuna. Duk wanda yake da nadin zama shugaban kasa, Allah zai sa shi shugaban kasar Najeriya.” Inji Oye yayin wani taron manema labarai na jam’iyyar APGA a Abuja.