Kocin Manchester United, Erik ten Hag, zai nemi siyar da Harry Maguire a bazara mai zuwa yayin da yake ci gaba da sake gina kungiyar.
A cewar The Guardian, United za ta yi la’akari da tayin da za ta yi wa kyaftin din na ta, a wani yunkuri na tara kudin siyan wasu yan wasan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sadio Mane ya shiga tawagar ƙasar Senegal don zuwa Qatar 2022
Da yuwuwar su yi babban asara wurin siyar da dan wasan saboda sun kashe wurin fam miliyan 80 kan dauko Maguire a watan Agusta 2019.
Maguire zai je gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar bayan wasan United da Fulham ranar Lahadi.
Ana sa ran dan wasan mai shekaru 29 a duniya zai zama cikin yan wasan zabi na farko ga Gareth Southgate yayin da Ingila za ta kara da Iran a wasan farko a ranar 21 ga watan Nuwamban shekarar nan.
Mai tsaron bayan ya fara wasa daya ne kawai ga Ten Hag tun lokacin da yake cikin jerin wasannin da kungiyar ta sha kashi a hannun Brighton da ci 2-1 a farkon kakar wasa ta bana da kuma wulakanci da United ta sha a hannun Brentford da ci 4-0 a watan Agusta.
An ce Ten Hag yana sha’awar ƙwararrun Maguire, amma rashin saurin sa bai burge shi ba kuma yana neman ƙarin gasa a wannan matsayi.
An ruwaito cewa Yeg Hag ya yaba da kwarewar Maguire amma sanyin jinkinsa ya sa yake son sayar da shi sannan yana bukatar Gasa a Bangaren Masu tsaton bayan United.
A WANI LABARIN KUMA: Kotu Ta Soke Takarar Wasu Yan APC 16 A Jihar Rivers
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas, a ranar Juma’a, ta kori ‘yan takarar APC 16.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Yan takarar na neman kujerun majalisar dokokin jihar a karkashin jam’iyyar APC