An bayyana Filato, Benue da Nasarawa a matsayin Jihohin da aka fi samun matsalar safarar mutane a Najeriya. Kamar Yadda Daily Trust ta ruwaito.
An bayyana hakan ne a ranar Asabar ta bakin masu magana a Taron farko na bikin Baje Kolin fina-finai na Kasa Da Kasa da ake kira Rock International Film Festival (RiFF) da kungiyar Jos Film Initiative (JOFII) ta shirya a Jos, babban birnin jihar Filato.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yuwuwar Kai Hare-Hare: Yanzu Yan Kasar Mu Zasu Iya Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja— Birtaniya
A yayin taron na RiFF, An ba da dama na musamman ga dalibai da matasa masu shirya fina-finai waɗanda fina-finan su suka yi tsokaci game da al’amuran zamantakewa da ‘yancin ɗan adam kuma suka duva al’amuran da suka shafi cikin gida da na duniya.
An shirya taron ne na RiFF mai jan hankali inda ake gudanar da laccoci/tattaunawa, tambayoyi da amsoshi daban daban.
Hakazalika, an baje kolin zane-zane da hotuna a cikin taron na kwanaki hudu.
A yayin zaman tattaunawar, mambobin kwamitin sun bayyana cewa fataucin mutane ya dauki wani sabon salo a Najeriya, inda Jihohin Filato da Benue da Nasarawa lamarin ya fi kamari.
A WANI LABARIN KUMA: Sojojin ruwan Najeriya sun ceto ma’aikatan jirgin 10 da ya kife a Legas
Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya (NNS) BECROFT ta ceto ma’aikatanta 10 daga wani jirgin kamun kifi a Legas.
Jirgin kamun kifi wani jirgin ruwan kamun kifi ne na kasuwanci da aka ƙera don kamo kifi a ruwa.