Daga Sabiu Musa Kano
Wata matashiya ta kashe yayanta mai Suna Sani Sulaiman har lahira a Unguwar Badawa ta jihar Kano, inda ta caka masa wuka a makogwaro sakamakon cacar baki da ta Kaure Tsakanin su.
A daidai lokacin da ake cikin Hada-hadar daura Auren daya daga cikin kannan sa a gobe lahdi.
Baki ne Makare da Gidan Ko ta Ina Jama’a ne ke Bulbulowa zuwa Wajen domin Tayasu Murnar Wannan Aure Yayin da wasu kuma Ke Kallon Kayan Akwatin Amarya kamar Yadda ya ke A al’adance.
Kawai ba ai Aune ba sai dai aka ji Sani ya Tsala wani Abun Ihu, yana Fadin Ku Taimaka min Zan Mutu ta Soke ni da Wuka, nan fa Gaba daya hankali ya dawo Kansu.
Inda Kowa ya kama Fadin Albarkacin Bakin sa an yi yunkurin Kai Sani, Asiniti amma Ina Karshe dai Rai yayi halin sa.
Yanzu haka dai an Dage Auren Ummi da Sadi Sani Maihakuri, har Illah Masha Allah, Saboda Zaman Makoki.