Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta tarayya ta ce ta kama masu tuka babura ba bisa ka’ida ba sama da 13,000 tare da kama babura kusan 20,000 a fadin kasar nan cikin watan Agusta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja kan shirye-shiryen gudanar da ayyukan kula da hatsari a watannin da suka gabata, mukaddashin hukumar FRSC Corp Marshall, Mista Dauda Biu, ya bayyana cewa ta kuma sanya sama da 100,000 cikin ma’ajin bayanan tantance ababen hawa na kasa.
Gidan talabijin na channels ya rawaito, A cewar Mista Biu, rundunar ta shirya gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a wuraren da jama’a ke taruwa kamar wuraren ajiye motoci a kan guje wa cunkoson ababen hawa da kuma wuce gona da iri a cikin wasu watanni.
“Daga cikin kokarin da muka yi wajen samun ingantaccen tattara bayanai shi ne ayyukan tabbatar da tsaro na musamman kan baburan da ba su da rajista wanda ya fara a farkon watan Agusta,” in ji Mista Biu.
“Shirin, wanda ya dace da umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ko shakka babu zai kara habaka bayanan kasa da kuma inganta tattara bayanan sirri da kuma bayanan laifuka a yayin da ake ci gaba da yaki da rashin tsaro a kasar”.
A wani labarin kuma: Okada: Masu Laifin Na Fuskantar Daurin Shekaru Uku, In Ji Gwamnatin Legas
Wadanda suka saba dokar hana zirga-zirgar babura kasuwanci na Achaba (Okada) a jihar Legas suna fuskantar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari saboda fara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar a ranar Juma’a.
Hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinan Sufuri na Jihar Legas, Dokta Frederic Oladeinde, wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Ikeja. Ya ce kashi na biyu na dokar hana okada a kananan hukumomi hudu da kuma kananan yankunanan shida.