Sanata 1 daya rage a PDP Kola Balogun ya canja Sheƙa zuwa APC a Oyo
Sanata Mai Wakiltar Oyo ta Kudu a Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Kola Balogun ya canja sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.
Balogun Wanda ya Kasance Olubadan na Ibadan, shi kaɗai ne aka zaɓa a Majalisar Dattijan Najeriya Jam’iyyar PDP a Oyo a Shekarar 2019.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Manchester City Ta Yi Wuff Da Haaland
Sanatan ya canja sheƙa ne daga PDP bayan Seyi Makinde ya miƙa Tikitin Tsayawa Takara na PDP na yankin Oyo ta Kudu ga Joseph Tegbe, wanda ya canja sheƙa daga PDP zuwa APC.
Sanata Balogun tuni yaje Sakatariyar PDP ta Ibadan tare da Sanata Teslim Folarin wanda ya shirya domin ayyana Takarar shi ta Gwamna a taron.
A wani Labarin Masarautar Olubadan ta nesanta kanta da abinda Ɗan gidan Basaraken yayi Femi, wanda ya ziyarci Tegbe domin neman goyon baya akan Takarar shi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Fadar ta fitar.