Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya jajanta wa wani shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a daren jiya yana da shekaru 73 a duniya.
A cikin sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, Sanata Barau ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da gwamnatin jihar Kano da daukacin al’ummar musulmi.
Karanta nanFG ta Shirya Samar da Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musamman Kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Ya ce gadon marigayin zai ci gaba da haskakawa, yana haskaka hanyar ilimi da ruhi ga kowa.
Sanarwar ta ce Sheikh Yusuf Ali shahararren malamin addinin Islama ne wanda tasirinsa ya wuce iyakokin kasa, inda ta kara da cewa koyarwarsa da hikimar sa sun wadatar da rayuwar mutane marasa adadi a Najeriya da ma wajenta.
Ya ce zurfafan iliminsa da wa’azinsa da rubuce-rubucensa sun kasance haske ne mai shiryarwa da zaburarwa ga musulmi da kuma jajircewarsa na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’ummar musulmi, zai bar tarihi da ba za a taba mantawa da shi ba ga tsararraki masu zuwa.
A wani labarin kumaAn Rasa Rayuka Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Bude Wuta A Wajen Taron Mauludi A Katsina
A yayin da muke alhinin tafiyarsa, ina rokon Allah, Mai rahama, Ya ba shi matsayi a Jannatul Firdausi, ya kuma azurta iyalansa da ikon jure wannan babban rashi. Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da su,” inji Sanatan.
Barau ya kara da cewar wannan mutuwa ba kawai ta iyalin malam bace mutuwa ce ga kaftanin musulmin Nijeriya da sauran kasashe.