Dan takarar shugaban kasa a babban zaben shugaban kasa da ya gabata a karkashin inuwar jam’iyar LP Peter Obi ya yi tsokaci game da yiwuwar tsayawarshi takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Obi ya bayyana haka ne a lokacin da yake yaba wa matasan Najeriya bisa goyon bayan da suka bayar a zaben shugaban kasa na 2023 inda ya kira matasa a matsayin kashin bayan cigaban Nijeriya.
Karanta nanFG ta Shirya Samar da Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musamman Kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Ya yi magana ne a wani taron manema labarai na duniya a Abuja, inda ya soki Kotun Koli kan tabbatar da zaben Shugaba Bola Tinubu.
Obi ya lura cewa hukuncin kotun kolin ya karya kwarin gwiwar da ‘yan Najeriya ke da shi a bangaren shari’a ya kuma bayyana karara cewar ‘yan Nijeriya basuda wani kwarin gwuiwa idan aka yi maganar shari’a.
A cewar Obi, hukuncin ya kawo karshen neman yin adalci a kan gudanar da zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
Ya ce karfin matasan Najeriya ya isa ace suna zaben shugaban kasar da suke bukata amma kotu ta hana masu damarsu,kuma ina so in tabbatar musu da cewa wannan ba shi ne karshen tafiyarmu ba amma ita ce mafari.
A wani labarin kumaAn Rasa Rayuka Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Bude Wuta A Wajen Taron Mauludi A Katsina
Za mu daure, mu dage har sai mun isa inda za mu yi domin Najeriya daya ce makomarmu kuma dole ne mu yi duk abinda zamu iya wajen ganin Nijeriya da ‘yan Nijeriya sun samu abinda suke bukata inji Obi.
za mu ci gaba da neman kuri’un ‘yan Najeriya domin su ma suna son a samu gwamnatin da ta dace da kishin mulkin su da kawo ci gaba ga al’umma.