By Abbas Yakubu Yaura
Sanata Uba Sani yace naji radadi matuka tare da tausayawa iyalan wadanda suka rasu, sannan Ina mika sakon ta’aziyyata zuwa gare su, Na kuma umurci jami’an dake kula dasu, da su gaggauta basu taimakon da ake bukata a gare su.
Baya da haka na kuduri aniyar yin duk abin daya wajaba akaina don ganin na tallafawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma kauyukan Giwa inda wadannan makiya bil’adama ke aikata munanan ayyukansu.
Sanata Uba Sani yayi wannan magana ne a lokacin da yake nuna alhinin sa kan kisan da ‘yan ta’adda suka yi a karamar hukumar Giwa akan al’ummar yankin sa,Lokacin Dayake jajantawa Sanatan yana mai cewa zuciyata na zubar da hawaye a kan mutanen mazaba ta 38 da aka kashe wadanda da basu ji ba ba su gani ba, a cikin hare-haren wuce gona da iri da ‘yan ta’adda suka kai a karamar hukumar Giwa.
Sannan yace Kauyukan da abin ya shafa an kashe rayuka tare da lalata dukiyoyi masu tarin yawa ba tare da nuna tausayi ba a cikin kauyukan Ruheya, Kauran Pawa, Marke da Idasu Gari.
Sannan Sanatan ya Kara da cewa Ina kira ga jami’an tsaro dasu dauki wannan sabon Hari a matsayin cin mutuncin jama’a tare da kuma magance wadannan munanan abubuwa na marasa kishin jama’a dake yiwa al’umma kisan gilla, Ku kai musu farmaki Kada ku basu sararin shakar numfashi domin Ba sa cikin al’umma mai wayewa irin tamu.
A karshe Sanatan yayi addu’ar Allah ya gafarta musu kurakuren wadanda abin ya shafa, ya basu Aljannar Firdausi