Daga Ibrahim Khalid
Sanatan Bauchi ta Kudu, Lawan Yahaya Gumau ya gangwaje kungiyoyin adininai a mazabarsa da filla-fillan motoci guda 27 kyauta domin agaza wa harkokin sun a yau da kullum.
Kungiyoyin da suka hada da Jama’atul izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunnah, Reshen Darikar Tijjaniyya, da reshen kungiyar Addinin Kirista ta Kasa (CAN), kazalika da Jama’atul Nasril Islam (JNI) da suke mazabar Sanatan ne suka amfana da wannan rabon da aka gudanar a jiya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabiyar wanda ya gudana garin Magama Gumau, Sanata Lawan Gumau ya shaida cewar yayi hakan ne domin tabbatar da rabar da ribar demokradiyya a tsakanin jama’an da suka zabeshi, yana mai cewa bayan ya baiwa bangarorin addinin, nan kusa su ma ‘yan siyasa za su amfana da tallafinsa matuka.
Wanda ke jawabi ta bakin wakilinsa, Alhaji Aminu Abubakar Dawaki wanda kuma shine Daraktan yakin zaben Sanatan, ya bayyana cewa Sanata Gumau wanda ya himmatu wajen inganta rayuwar jama’an da yake wakilta.
Dawaki, wanda ya yi la’akari da cewar, fagen siyasa a share yake tarwal wa Sanata Gumau wanda ya inganta rayuwar dubban jama’a ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa kamar rijiyoyin burtsatse, ajujuwan makarantu, wutar lantarki, karfafa mata da matasa, samar wa matasa ayyukan soji, dan-sanda, kastam, imagireshin, dogarancin hanya, da samar wa matasa makarantu, dadai sauran su.
Alhaji Aminu Dawaki, don haka ya yi kira ga daukacin jama’ar mazavar sanatan dake cikin kananan hukumomin Bauchi, Toro, Alkaleri, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass da Bogoro da su baiwa Sanatan dukkan goyon baya da ya dace kan fafitikar sa ta tsamo jama’a daga kangin talauci, jahilci, cutattaki da kuma ‘yunwa.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, jagoran kungiyar JIBWIS a karamar hukumar Toro, Muhammad Abdullaji Jajuwal ya jinjina wa Sanata Lawal Gumau wanda, ya ce, yana tallafawa kungiyoyin addinai dake cikin karamar hukumar, don haka ya yi masa fatar alheri.
Rabaran Jaja S. Dangi wanda tsohon jami’i ne a hukumar jin dadin masu Urshalima da yake cikin kungiyar addinin kiristanci a karamar hukumar Toro da suka amfana da tallafin, wanda kuma ya yabawa Sanata Gumau bisa wannan tagomashi, yana mai cewar, motar zata taimaka wajen gudanar da lamuran addinin su.
Shugabannin kungiyoyin wadanda suka bayyana cewar, ko Baburan hawa ba su da shi, yayin da suka samu kyautukan motoci, sai suka nuna farin cikin su bisa wannan alfarma da aka yi masu, tare da yiwa sanatan addu’ar Allah ya ja likafar sa zuwa kujerar gwamna.
Malam Abdulrahman Abubakar Ghani, wani jagoran JIBWIS a garin Liman Katagum dake cikin karamar hukumar Bauchi ya yi la’akari da cewar, kowace jam’iyyar siyasa mutum yake ciki ko goyon baya, babu shakka yana cikin daya daga cikin manyan addinan nan guda biyu, walau Musulumci ko Kiristanci, don haka tallafawa addinan nan biyu ya yi daidai.