Rahotanni daga Abuja na bayyana cewa a halin yanzu dai shugabancin majalisar dattawan na tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro.
An fara taron ne ‘yan mintoci da karfe 2:00 na rana a harabar majalisar dattawa ta kasa a ranar Laraba.
Wasu Sanatocin da suka halarci taron sun hada da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Wamakko; Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojojin Ruwa, George Sekibo; da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Abdullahi DanBaba.
DUBA WANNAN LABARIN: An samu Ambaliyar ruwa a karamar hukumar Warawa
Har kawo wannan lokacin hada rahoton, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba duk da cewa ya zo ne da misalin mintuna 15 kafin karfe 2 na rana cikin tsauraran matakan tsaro.
Sai da aka jinkirta taron don zuwansa, kuma idan dai za a iya tunawa, ‘yan majalisar adawa sun baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari wa’adin makonni shida ya warware matsalar rashin tsaro a kasar ko kuma a tsige shi.