Sanatocin Arewa: ‘Yan Majalisu 58 Sun Koka Kan Rashin Adalci A Kasafin Kudin 2024
‘Yan majalisar 58 a karkashin kungiyar Sanatocin Arewa, sun yi zargin cewa hasashe da tanadin kasafin N28.7tn 2024, rashin adalci ne ga Arewa.
Sun kuma yi zargin cewa ana mayar da wasu hukumomin tarayya zuwa Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tinubu ya ba da sabon umarni kan lamunin ɗalibai
Sai dai Sanatocin Arewacin kasar, sun ce sun dukufa wajen ganin sun magance matsalolin da tunanin al’ummar mazabarsu a Arewa dangane da kudiri da manufofin da Gwamnatin Tarayya ta gindaya.
Sanatocin sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun su, Sanata Suleiman Kawu Summaila (NNPP Kano ta Kudu) ya sanya wa hannu a ranar Litinin a Abuja mai taken “Rarraba Kudade a Kasafin Kasa na 2024 tare da mayar da wasu Hukumomin Tarayya Legas.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A matsayinmu na wakilan jama’a a matakin kasa (Majalisar Dattawa), mun himmatu wajen ganin mun magance damuwa da jin dadin al’ummar mazabarmu dangane da wasu shawarwari da manufofin da gwamnatin tarayya ta gabatar.
“Sai kuma tabarbarewar rarrabawa da rabon kayan aiki a cikin kasafin kudin 2024, mayar da wasu hukumomin tarayya daga Abuja zuwa Legas.
“Mun fahimci mahimmancin samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnati da ‘yan kasarta, kuma a cikin wannan ruhi ne muke sanar da kokarin mu na hadin gwiwa wajen neman sasantawa cikin lumana a kan wadannan matsalolin da ke damun su, a cikin tsarin tsarin mulkin mu da dokokin da ake da su.
“Da farko, mu tabbatar wa ‘yan mazabarmu cewa mun dauki damuwarsu da muhimmanci kuma muna yin hadin gwiwa da abokan aikinmu don magance wadannan al’amura yadda ya kamata. Mun yi imani da karfin tattaunawa da hadin gwiwa wajen kawo sauyi mai kyau ga al’ummarmu.”
‘Yan majalisar na Arewan sun kara da cewa, “Mun yi imani da karfin tattaunawa da hadin gwiwa wajen kawo sauyi mai kyau ga al’ummarmu.
“Mun fahimci mahimmancin rawar da muke takawa a matsayin gada tsakanin jama’a da gwamnatinsu, kuma tare da babban nauyi da jajircewa muka gudanar da wannan aiki.
A wani labarin kuma:Dagaske Tinubu yana kula da ƙalubalen Najeriya – CAN
Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya ce a jiya gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu na yin kokari mai kyau na tinkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.
Shugaban na CAN ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar shugabannin kungiyar a ziyarar ban girma da suka kaiwa shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.