Igbo ne za su tantance shugabancin ku kan yadda kuke tafiyar da Nnamdi Kanu – Ejimakor ga Tinubu
Aloy Ejimakor, mashawarci na cmusamman ga Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, a ranar Talata ya bayyana yadda ‘yan kabilar Igbo za su ayyana matsayin shugaban kasa Bola Tinubu.
Ejimakor ya bayyana cewa ‘yan kabilar Igbo za su ayyana Tinubu ta yadda ya tafiyar da lamarin Kanu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dagaske Tinubu yana kula da ƙalubalen Najeriya – CAN
Da yake wallafawa a kan X, ya gargadi shugaban kasa kan barin miyagu su sanya shi cikin turbar rikicin siyasa da ‘yan kabilar Igbo.
Ya rubuta: “Ga Ndigbo, za a bayyana shugabancin Tinubu ta yadda zai tafiyar da al’amarin MAZI NNAMDI KANU. Duk wanda ya gaya wa Tinubu in ba haka ba, to ya yi ɓarna ne kuma ya sa shugaban ƙasa ya shiga tafarki na rikicin siyasa da Ndigbo. Ku yi imani da shi ko a’a, #MNK na daya daga cikin jiga-jigan Ndigbo.”
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da ya kai gwamnatin Najeriya gaban majalisar sarakunan Burtaniya kan ci gaba da tsare Kanu.
Ejimakor ya bukaci majalisar sarakunan kasar Birtaniya da ta sa baki kan azabtarwa, dauri da kuma tsare Kanu da gwamnatin Najeriya ke yi.
A cikin wata takardar koke ga kwamitin kula da harkokin kasa da kasa da tsaro na majalisar dokokin kasar, ya bukaci majalisar dokokin Birtaniya da ta sanya wa gwamnatin Najeriya takunkumi idan ta gaza sakin Kanu ba tare da wani sharadi ba tare da mayar da shi kasar Birtaniya.
A wani labarin kuma:Sanatocin Arewa: ‘Yan Majalisu 58 Sun Koka Kan Rashin Adalci A Kasafin Kudin 2024
Yan majalisar 58 a karkashin kungiyar Sanatocin Arewa, sun yi zargin cewa hasashe da tanadin kasafin N28.7tn 2024, rashin adalci ne ga Arewa.
Sun kuma yi zargin cewa ana mayar da wasu hukumomin tarayya zuwa Legas.