An bukaci majalisar dattijai da ta gaggauta amincewa da kudirin dokar kafa kwalejin nazarin kasa da siminti a garin Iselu da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.
Kudirin da ya samu nasarar yin karatun farko a majalisar dattawa a ranar 5 ga watan Oktoba, Sanata mai wakiltar Ogun ta Yamma, Olamilekan Adeola ne ya dauki nauyinsa.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa karamar hukumar Yewa ta Arewa na jihar Ogun na daya daga cikin yankunan da ke da tarin duwatsu da sauran albarkatun kasa.
Karamar hukumar tana karbar bakuncin daya daga cikin masana’antar siminti mallakar rukunin Dangote a yankin Ibese.
Karanta nanZanga Zanga Ta Barke A Jahar Nasarawa Bayan Umarnin Kotu Na Sauke Gwamna Sule Daga Kujerarsa
Da yake jawabi, mambobin kungiyar Ketu Advancement Forum (KAF), a ranar Litinin din da ta gabata sun bukaci Adeola da ya yi duk mai yiwuwa don ganin cewa majalisar dattawa da ta wakilai sun goyi bayan amincewa da kudirin cikin gaggawa.
Muna rokon ku da ku tura dukkan sahihancin ku na majalisa wajen hada kan ‘yan majalisun tarayya guda biyu don nuna goyon baya ga gaggawar zartar da kudirin dokar da kuma kafa Kwalejin,” in ji kungiyar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Kodinetan ta Kunle Abiose da Sakatare-Janar, Dotun Adeleye.
Kungiyar ta yabawa Adeola, tana mai cewa wannan ya fi dacewa da kasar Iselu da Ketu dake da yawan ma’adinan farin karfe, wanda shine mafi girma a Najeriya.
Ya ce ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya samu amincewar shugaban kasa ya fara amfani da hanyoyin siminti/kankare a fadin kasar nan. Wannan ya biyo bayan dimbin fa’idojin da titunan siminti ke da su kan hanyoyin da aka gina da kwalta.
A wani labarin kumaTallafin Gwamnati Ga Magidanta Miliyan 15 Zai Fara 17 Ga Watan Oktoba-Ministar Walwala
Wannan sabuwar taswirar za ta kara yawan bukatar siminti a kasar nan; don haka akwai bukatar Injiniyoyin da za a bukata a cikin manyan masana’antar siminti.
Muna sake gode wa Majalisar Dattawan nan da muke sa ran za a gaggauta amincewa da kudirin da zai tallafa wa Hukumar Zartarwa ta Tarayyar Najeriya don karkatar da tattalin arzikin kasar daga danyen mai zuwa sauran albarkatun ma’adinai domin ci gaban kasarmu ta Najeriya inji shi.