- Yanzu haka dai ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa za su gana a ranar Larab kan yadda Isra’ila ke ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza
- Hakan na zuwa ne ya yin da ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta bukaci taron gaggawa na matakin ministoci na kungiyar hadin kan Larabawa
- Taron da za a yi, zai nemi nemo “hanyoyin aiwatar da harkokin siyasa a matakin Larabawa da na kasa da kasa
Yanzu haka dai ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa za su gana a ranar Laraba domin tattaunawa kan yadda Isra’ila ke ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza bayan harin ba-zata da Hamas ta kai kan Isra’ila, in ji kungiyar yankin.
Kungiyar Hamas ta kaddamar da Operation Al-Aqsa a ranar Asabar din da ta gabata, kuma ta ce harin ba zato ba tsammani ya faru ne a matsayin mayar da martani ga harin da aka kai a Masallacin Al-Aqsa da kuma karuwar tashin hankalin mazauna garin.
KARANTA WANNAN: Mutum 1,000 Sun Rasa Ransu Yayinda Ake Cigaba Da Fada Tsakanin Falasdinu Da Isra’ila
Hamas ta ce ta harba rokoki tare da kame ‘yan Isra’ila da dama.
Taron da za a yi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Eygpt, zai nemi nemo “hanyoyin aiwatar da harkokin siyasa a matakin Larabawa da na kasa da kasa”, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza bayan harin na ranar Asabar, in ji mataimakin babban jami’in kungiyar kasashen Larabawa Hossam Zaki a cikin wata sanarwa.
Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu a ranar Asabar, ta bukaci taron gaggawa na matakin ministoci na kungiyar hadin kan Larabawa, kan sabon tashin hankalin da Isra’ila ta yi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce ta umurci tawagarta ta dindindin zuwa kungiyar kasashen Larabawa da ta bukaci taron gaggawa na majalisar kungiyar a matakin ministoci.
An cimma wannan ci gaban ne a kan “Haɓakar zaluncin da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu,” in ji shi.
Ma’aikatar harkokin wajen Morocco a ranar Lahadi, ta kuma yi kira da a gudanar da taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa a matakin ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa don “Shawarwari da hadin kai kan tabarbarewar al’amura a zirin Gaza da kuma barkewar ayyukan soji da ke auna fararen hula.”
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, ana ci gaba da tuntubar juna sosai kan taron da za a gudanar a wannan makon a hedkwatar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da ke birnin Alkahira.
A wani labarin kuma, Tallafin Gwamnati Ga Magidanta Miliyan 15 Zai Fara 17 Ga Watan Oktoba-Ministar Walwala
Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu ta ce gwamnatin tarayya za ta kaddamar da shirin mika kudi ga gidaje miliyan 15 a ranar 17 ga Oktoba, 2023.
Edu ta bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Television na Sunday Politics.