By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce marigayi Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi lll, ya wakilci al’adun gargajiya na babbar Daular Oyo musamman kabilar Yarbawa baki daya.
Lawan, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, a ranar Lahadi a Abuja, ya bayyana rasuwar Oba Adeyemi a matsayin babban rashi ga kabilar Yarbawa a gida da waje, da kuma Najeriya baki daya.
Don haka shugaban majalisar dattawan ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Oyo da daukacin kabilar Yarbawa bisa rashin wani babban basaraken gargajiya na Afirka.
Oba Adeyemi ya wakilci al’adun gargajiya na kabilar Yarbawa da kuma tarihin Oyo, daya daga cikin mafi girma a Afirka, musamman kudancin Sahara.
“Oba Adeyemi, a tsawon mulkinsa, ya bayar da gudunmuwa matuka wajen ci gaban rayuwar jama’a da ta jiki a tsohuwar Jihar Yamma, Jihar Oyo da ma Nijeriya baki daya, walau a karkashin mulkin soja ko a tsarin dimokuradiyya mai tasowa.
“Ya yi hakan ba kawai a matsayin mai kula da tarihin Yarbawa ba, har ma a matsayinsa na masani mai zurfin ilimi da hikima.
Oba Adeyemi, a ranarsa ta karshe a kan karagar mulki, ya samu karramawa da girmamawa ga kujerar Alaafin na Oyo saboda yadda ya baje kolin darajar Cibiyar.
Za a yi kewar muryarsa ta hikima daga talakawansa, ’yan uwansa sarakunan gargajiya, gwamnatoci da jama’a a duk fadin Nijeriya.
“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, al’ummar jihar Oyo, daukacin kabilar Yarbawa da ‘yan Najeriya baki daya bisa rashin wani babban basaraken gargajiya na Afirka da yi masa fatan alheri,” in ji Lawan.
Comments 1