A yayin da kasar nan ke fama da kalubalen tattalin arziki, mai martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya yi kira ga ‘yan kasuwa a jihar da su yi wa talakawa saukin kayayyaki.
Sarkin wanda ya damu da tashin farashin kayayyakin masarufi a Jihar, ya roki ‘yan kasuwar da su kara wa jama’a kayan masarufi da araha, musamman ma masu karamin karfi.
Karanta nanAn Rasa Rayuka Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Bude Wuta A Wajen Taron Mauludi A Katsina
Ya jaddada cewa riba mai yawa, musamman kan abubuwa masu mahimmanci kamar abinci, ya saba wa ka’idodin ɗabi’a.
Sarkin ya yi wannan roko ne a ranar Litinin yayin da ya ziyarci kasuwanni daban-daban a cikin babban birnin Bauchi domin tantance yanayin farashin da ake ciki.
Adamu, wanda kuma yake rike da mukamin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Bauchi, ya yi nuni da irin halin kuncin da marasa galihu ke fuskanta, musamman fafutukar da suke yi na samun kayan abinci.
Ya shawarci ’yan kasuwa da su binciko hanyoyin da za su sa farashin su ya isa ga talakawa ba tare da an yi asarar kudi ba.
A wani labarin kumaRundunar ‘Yan Sanda Ta Bayarda Umarnin Rarraba Motoci Masu Sulke Ga Jahohi Uku
A nasu jawabin, ‘yan kasuwa da dama sun yabawa Sarkin bisa ziyarar da ya kai kasuwannin da kansa domin ganin yadda lamarin ke faruwa.
Sun yi alƙawarin kiyaye farashi mai ma’ana duk da ƙalubalen tattalin arziki, da tabbatar da cewa masu karamin karfi za su iya siyan kaya ba tare da matsananciyar damuwa ba.