By Abbas Yakubu Yaura
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga duk wani shiri da zai hada kan ‘yan kasuwar Gambiya da Najeriya musamman na jihar Kano ta hanyar huldar tattalin arziki domin samun ci gaban siyasa da zamantakewa a yammacin Afirka.
Da yake magana a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Gambia, Mista Adama Barrow, a ranar Litinin, sarkin ya ce lokacin kulla alaka ya zo “domin muna da jiragen sama na kai-tsaye tsakanin kasashenmu biyu.”
Sarkin ya sanar da shugaban kasar cewa Kano a matsayin jiha mafi yawan al’umma a Najeriya ta kasance babbar cibiyar kasuwanci tun shekaru aru-aru tun daga lokacin da ake kasuwanci a yankin kudu da hamadar Sahara.
Ya ce hakan ne yasa ya samu tawagarsa ta kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu da ma’adanai da kuma noma ta Kano da nufin ganawa da takwarorinsu na Gambia domin lalubo hanyoyin hadin gwiwa a tsakanin su.
Da yake mayar da martani, shugaba Barrow ya godewa sarkin bisa wannan ziyara da ya kai masa, ya kuma ba shi tabbacin cewa zai duba abubuwan da za su inganta tattalin arzikin Gambia da ‘yan kasuwan Najeriya, musamman na Kano, duba da dimbin kamanceceniya da ke tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Ya kuma yi nuni da cewa, ziyarar za ta taimaka matuka wajen samar da siminti da inganta ‘yan uwantaka a yankin Afirka ta Yamma da ma bayanta.