By Abbas Yakubu Yaura
Masarautar Minna ta dakatar da Hakimin Allawa da ke karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, Malam Bello Haruna, kan yin auren dole da kuma wani aiki na rashin biyayya.
Masarautar a cikin wata wasika da mataimakin sakatarenta Usman Umaru Guni ya aikewa da wakilinmu, ta ce basaraken ya auri wata yarinya da karfi da yaji (wacce a sakaya sunanta), ya wulakanta mahaifinta sannan kuma ya umurci ’yan banga dasu yi masa duka.
An kuma zargi Hakimin gundumar da rashin biyayya ga rashin amsa kiran da fadar ta yi masa na bayyana wasu korafe-korafen da ake yi masa.
Sarkin ya ce dabi’un basaraken sun nuna shi a matsayin rashin halayen jagoranci domin zaman lafiya da ci gaban al’ummar da aka nada shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa masarautar ta bayyana Galadima Allawa, Ahmadu Magaji a matsayin sabon hakimin riko.