By Abbas Yakubu Yaura
Shahararren mai bada maganin gargajiya Dakta Simon Odo wanda aka fi sani da ‘Sarkin Shaidan’ wanda kuma ya auri mata 59 da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa marigayi Odo wanda ya fito daga yankin Aji, a karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa a jihar Enugu ya rasu ne a ranar Talata bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Dan sa, Emeka Odo, wanda ya tabbatar da rasuwarsa, yace an fara shirin bikin binne shi.
Sannan ya kara da cewa , “Sarkin Shaiɗan ya rasu, da sanyin safeyar talata, bayan yasha fama da gajeriyar rashin lafiya ta kusan makonni uku.
Kazalika dan nasa yace “Muna yin taron dangi don yin cikakken tsarin binne shi yayin da ya bar umarni cewa kada mu sanya shi a dakin ajiyar gawa.”
Tun bayan da aka samu labarin rasuwarsa masu ta’aziyyar da ‘yan uwa sun yi ta taruwa zuwa gidan sa.