Ministan harkokin waje Saudiyya, Faisal bin Farhan ya ce kasarsa za ta sake bude ofishin jakadancinta a Qatar a matsayin wani bangare na yarjejeniyar maido da huldar diflomasiyya a tsakaninta da makwafciyarta don kawo karshen gutsiri tsoma da suka shafe shekaru uku su na yi.
Ministan ya ce Saudiyya za ta maido da cikakkiyar hulda da Qatar kamar yadda kasashen 2 suka amince a tattaunawarsu ta farkon wannan wata, kuma a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za a sake bude ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Doha.
Ya kara da cewa babu wani abin da zai kawo tsaiko a game da aniyar tasu, sai dai watakila matsaloli da suka shafi zirga zirga.
A watan Yunin shekarar 2017, Saudi Arabia da abokanta, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka kakaba wa Qatar takunkumin da suka hada da haramta mata shawagi a srarain samaniyarsu bisa zargin cewa tana taimaka wa kungiyoyin ‘yan ta’adda, da kuma abotan da take da Iran.