Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar a ranar Lahadi cewa ‘yan bindiga sun kashe wata tsohuwa mai shekaru 80 da wasu mutane hudu a wasu hare-hare daban-daban a wasu sassan jihar.
Mista Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.Ya ce an kashe tsohuwar ne lokacin da ‘yan fashin suka far wa kauyen Sharu da ke karamar hukumar Igabi na jihar inda suka afkawa gidaje da dama.
Yayin da suke harbin kan mai uwa da wabi, Hauwa Umaru, 80, harsashi ya same ta kuma ta rasu nan take. A wani lamarin kuma,‘yan bindiga sun kashe Hakimin Konti a karamar hukumar Chikun. Haka kuma a karamar hukumar Chikun,‘yan bindiga sun kashe wasu mazauna yankin a Dande.
A karamar hukumar Giwa,‘ yan bindiga sun tare hanyar tsakanin Fatika da Kidandan sannan suka bude wuta kan matafiya da ke bin hanyar. Kwamishinan ya ce “Har ila yau mace guda da ba a san ko wace ce ba ta rasu, sannan wasu mutum uku sun jikkata a harin.”
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir el-Rufai, wanda ya nuna bakin ciki game da hare-haren, ya jajantawa dangin mamatan tare da yin addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a hare-haren.
Aruwan ya ce gwamnan ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da sahihan bincike kan abin da ya bayyana a matsayin abubuwan da ke faruwa