A ranar Asabar din da ta gabata ce masarautar Saudiyya ta bayyana cewa ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 81 da aka samu da laifi.
Sanarwar ta ranar Asabar ita ce kisa mafi girma da kasar ta yi a tarihinta na zamani – fiye da kisa 67 da aka bayar da umarnin au a cikin 2021 da 27 a cikin shekarar 2020.
Kafin ranar Asabar, wannan shine kisa mafi girma a tarihin kasar tun shekarar 1980, sai na shekrra 2016 lokacin da aka kashe mutane 47.
Sai dai alkalumman na baya-bayan nan ya zarce na shekarar 1980 lokacin da aka kashe ‘yan bindiga 63 a wani hukunci da Mahukunta Kara su ka yi.
Kazalika Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya bayar da rahoton cewa, mutanen 81 an same su da laifin ta’addanci da kuma aikata manyan laifuka.
Daga bisani Kuma rahotanni sun yi nuni da cewa, wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da ‘yan kungiyar al-Qaeda, ISIS da masu goyon bayan ‘yan tawayen Houthi na Yemen.
Daga cikin mutane 81 da aka kashe, 73 ‘yan kasar Saudiyya ne, bakwai ‘yan Yemen ne, daya kuma dan kasar Syria ne.
“Wadannan mutane da adadinsu ya kai 81, an same su da laifuffuka daban-daban da suka hada da kashe maza da mata da kananan yaran da ba su ji ba ba su gani ba,” in ji kamfanin labaran kasar Saudiyya SPA, a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar.
Comments 1