Jam’iyyar APC a jihar Sokoto, ta ce ta sake samun wasu jiga-jigan yan siyasa daga jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyar, gabanin babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Daily Nagerian ta ruwaito cewa, Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai ba da shawara na musamman ga Aliyu Wamakko ya raba wa manema labarai ranar Talata a Sokoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC Ta Sanya Ranar Da Za’a Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihohi Uku
A cewar Abubakar, wadanda suka sauya shekan sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni, wanda suka hada da magatakardan jam’iyyar PDP na shiyyar, Alhaji Musa da wasu shugabannin Jam’iyar a matakin Gundumomi.
Ya kara da cewa, sabbin mambobin sun samu tarba ne a wani dan takaitaccen taro da aka yi a garin Sabon Birni karkashin jagorancin Idris Gobir mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ahmad Aliyu.
Mista Abubakar ya ce, “yawan wadanda suka sauya shekan ya nuna cewa jam’iyyar mai mulki a jihar, ta kamo hanyar zama tarihi.”
Ya nanata kudurin APC na samar da ababen more rayuwa tare da hada kai da dukkan ‘yan jam’iyyar domin biyan bukatun al’ummar jihar baki daya.
Kazalika, da suke jawabi, Masu sauya shekar sun ce sun koma APC ne domin su ba da gudunmawar su domin samun nasarar APC a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Dukkannin Zabukan Fidda Gwanin Jam’iyar APC A Jihar Rivers
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Rivers ta soke dukkan zabukan fidda gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar.
Idan dai ba a manta ba wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC da ke biyayya ga Dan takarar Gwamna a jam’iyyar SDP, Sanata Magnus Abe, sun kai kara Kotu suna masu kalubalantar zaben fidda gwanin da aka yi a jihar tare da yin ikirarin cewa ba a yi zaben fidda gwani na yan takarar yan majalissar wakilai ba a jihar.