Majalisar dokokin jihar Rivers ta tantance tare da tabbatar da sunayen kwamishinoni 18. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Jaridar Dimokuradiyya a yau, ta ruwaito muku cewa, Gwamna Nyesom Wike ne ya mika sunayen Kwamishinonin ga majalisar a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sauya Sheka: Jam’iyar PDP Ta Kusa Zama Tarihi A Jihar Sokoto– Wamakko
Daga bisani an bukaci wadanda aka nada, da su bayyana a gaban majalisar a ranar Talata domin tantance su.
Wadanda aka nada sun hada da tsohon kakakin jam’iyyar APC a jihar Rivers Chris Finebone, wanda kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta Rivers
Da yake jawabi bayan kammala tantancewar, shugaban majalisar, Ikuyi Ibani, ya yi kira ga ‘yan majalisar da suka kada kuri’ar amincewa da dukkanin wadanda aka aiko da sunayen su kuma aka tantance su.
An bukaci wasu daga cikin wadanda aka nada da suka hada da tsohon dan majalisar tarayya, Jacobson Nbina da kuma tsoffin ‘yan majalisar zartarwa na jihar da su jinjinawa yan majalissar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan tabbatar da shi, tsohon kakakin jam’iyyar APC, Finebone, ya yi alkawarin yin aiki domin amfanin gwamnatin jihar ta Rivers da Al’ummar jihar baki daya.
A WANI LABARIN KUMA: INEC Ta Sanya Ranar Da Za’a Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihohin, Imo, Bayelsa Da Kogi
Za a gudanar da zaben gwamnonin jihohin Imo, Bayelsa da Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana.
Daily Post ta ruwaito cewa, Hukumar ta bayyana hakan ne a taronta na mako-mako a ranar Talata