Mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 sun amince da wani kudiri a jiya Talata domin mayar da hankali wajen bunkasa kekuna a matsayin wani makami na yaki da sauyin yanayi.
Kudirin da wakilin kasar Turkmenistan ya gabatar, an zartar da shi ne gaba daya, kuma dukkan kudurorin babban zauren majalisar, bai yi togaciya ga wannan kuduri ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su hada keken a cikin ababan zirga-zirgar jama’a, a birane da kauyuka a kasashe masu tasowa.
Ƙudurin ya lura cewa, haɓaka hawan keke ta hanyar ingantaccen tsaro na hanyoyi da inganta hawan keke zai taimaka wajen samun “ci gaba mai dorewa, ciki har da rage hayaki mai gurbata yanayi.”
Kudurin ya karfafa gwiwar kasashe mambobin kungiyar da su ba da kulawa ta musamman kan hawan keke a cikin dabarun raya kasa, da suka hada da ayyukan raba keke.
Kekunan dai, baya ga hayakin da ba sa fitarwa, an san su don haɓaka salon rayuwa mai kyau yayin da ake motsa jiki.
Haka kuma, idan aka yi la’akari da matsayin madadin, za a rage yawan cunkoson ababen hawa da kuma yawan zafin da ake samu sakamakon karuwar wasu ababen hawa.