Tsohuwar wadda ta lashe manyan kofuna huɗu cikin shekara ɗaya a gasar tennis ta duniya ‘Grand Slam’, Naomi Osaka ta sanar da cewa a tana ɗauke da juna biyu a halin yanzu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Osaka, ƴar asalin ƙasar Japan, wadda ta riƙe matsayi na ɗaya a jerin ƴan wasan tennis na duniya ta janye daga gasar ‘Australia Open’ a farkon wannan mako, kuma ba ta yi wasa ba tun watan Satumban shwkarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dandazon Jama’ar Da Suka Fito A Onitsha Ya Nuna Cewa, Peter Obi Ne Zai Lashe Zabe — COSEYL
Naomi Osaka ta ce “2023 za ta zamo shekara mai cike da darussa a gare ni”, sannan ta ce tana sa ran komawa harkokin wasan a shekarar 2024.
Ta ƙara da cewa “ɗaya daga cikin abin da na ƙagara na gani shi ne abin da zan haifa ya kalle ni ina fafatawa a gasa, sannan ya faɗa ma wani cewa ‘wannan ce mahaifiyata ce.”
Kazalika Osaka ba ta buga cikakken wasa ba tun bayan da ta sha kashi a zagayen farko a gasar US Open kuma ta halarci gasa 11 kacal a shekarar 2022.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Peter Obi Ya Isa Jihar Enugu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya isa Enugu domin gudanar da wani gangamin yakin neman zaben sa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Obi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter ranar Alhamis.
“Na isa birnin Enugu ne don taron gaggamin yakin neman zabe a,” ya rubuta.
A kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Anambra ya je jiharsa a ranar Talata, inda dimbin magoya bayansa suka tarbe shi.