Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Gombe, ta ce ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 15 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba.
Shugaban hukumar Aliyu Adole ya bayyana hakan a yayin wata hira da da manema labarai a garin Gwambe.
Ya ce hukumar ta kama mutanen ne da kilogiram 523 da 174 na miyagun kwayoyi, wanda a ciki akwai ganyen tabar wiwi.
Adole ya kara da cewa, abin takaici ne yadda mutane musamman matasa su ka koma ga noman ganyen tabar wiwi maimakon kayan abinci.
A karshe ya bukaci masu ruwa da tsaki da Malaman addini, su hada hannu da hukumar don ganin an wayar da kan matasa ilollin da ke tattare da yin tu’amalli da miyagun kwayoyi.