By Abbas Yakubu Yaura
Chiemeka Azinze, wanda ake zargin hamshakin attajirin nan mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya mutu a gidan yari.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Evans dai yana fuskantar shari’a tare da Joseph Emeka, Udeme Uping da Chiemeka Azinze, bisa laifin yunkurin sace shugaban kungiyar YSGM, Cif Vincent Obianodo.
Wadanda ake zargin dai suna fuskantar tuhume-tuhume bakwai da suka hada da kisan kai, yunkurin kisan kai, hada baki don yin garkuwa da mutane da dai sauransu.
A cewar takardar shaidar mutuwarsa da NAN ta samu a ranar Litinin, Arinze ya rasu ne da misalin karfe 9.08 na daren ranar Juma’a, sakamakon bugun zuciya.
Takardar shaidar mutuwar wadda babban asibitin Ajeromi, Ajegunle ya bayar, wanda Dokta B.E Salisu ya sanya wa hannu, ta nuna cewa marigayin wanda ya rasu yana da shekaru 45 a duniya, yana kuma fama da cutar kanjamau mai sarkakiya.
A cewar jami’an gidan gyaran halin da suka bukaci a sakaya sunansu ,sun ce Arinze, wanda ke fama da rashin lafiya, an garzaya da shi daga asibitin Kirikiri Maximum Correctional Centre zuwa Babban Asibiti, inda ya rasu acan.